Tsaro: El Rufa’i Bai Fahimci Inda Aka Sa Gaba Ba – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahu Umar Ganduje, ya yi zargin cewa takwararsa na jihar KadunaMalam Nasir El-Rufa’i, bai fahimci matsalar tsaron da Arewa ke fuskanta wanda hakan ya sanya shi ya fito ya yi wasu maganganun da zasu iya dagula al’amurra maimakon daidaita su.

Idan jama’a ba su manta ba Gwamna El-Rufa’i ya yi wani jawabi a hirarsa da sashin Hausa na BBC cewa babu hadin kai tsakanin gwamnonin Arewa wajen yakan matsalan tsaro.

Amma Ganduje a hirarsa da Rediyan Faransa ranar Alhamis, ya bayyana cewa ya taba magana da El-Rufa’i da gwamnan Bauchi kan yadda za’a magance matsalar tsaro wadda ta daɗe tana addabar yankin.

Ganduje ya ƙara da cewar shi yajanyo hankulansu bisa shawaran da jami’an tsaro suka bada kan yadda sauran jihohi yankin zasu amfana da dajin Falgore dake jihar Kano.

Ganduje ya ce gwamnatin Bauchi da Kaduna sun turo wakilansu wajen ganawa kan matsalar tsaro kuma sun tattauna da masana, wannan yasa jawabin El-Rufa’i ke bashi mamaki.

“Da farko dai maganar El Rufa’i na cewa akwai rashin hadin kai tsakanin gwamnoni ban san dalilin fadin haka ba. Jami’an tsaro sun bamu shawaran cewa Kano, Kaduna da Bauchi su turo wakilansu Kano domin tattaunawa kan magance matsalar dajin Falgore da kuma yadda tsagerun yan bindiga ke amfani da dajin,”.

“Na yi magana da gwamnan Kaduna da Bauchi kuma suka turo wakilai inda kowa ya bada gudunmuwarshi wanda al’ummar duniya sun shaida haka kuma akayi aikin aka samu nasara.

Ban fahimci maganar rashin hadin kai ba.” “A nawa tunanin, shi (El-Rufa’i) bai fahimci matsalar sosai ba. Saboda kowace matsalar tsaro ta danganta da sababi. Duk irin hadin kan da mukayi, dole salonmu ya banbanta.”

Labarai Makamanta