Tsaro: An Dakatar Da Zirga-Zirgan Jiragen Kasa A Najeriya

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya NRC, ta ce ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a ƙasar saboda tsaro.

NRC ta sanar da hakan ne a shafinta na intanet a ranar Alhamis da rana.

Hakan na zuwa ne bayan da aka kai wa wasu jiragen ƙasa na hanyar Abuja zuwa Kaduna hari har sau biyu a jere.

Harin farko ya faru ne a ranar Laraba da yamma kan jirgin da ke tafiya Kaduna daga Abuja, sai kuma hari na biyu da ya faru ranar Alhamis da safe a kan jirgi mai tafiya Kaduna daga Abuja.

Wasu da lamarin ya rutsa da su a cikin jirgin sun ce harin ya jawo lalacewar layin dogon da jirgin ke bi.

Sanata Shehu Sani wanda ke cikin fasinjojin jirgin kasan ya ce “a ranar Alhamis da safe an kai hari kan jirgin kasa, sannan da yammacin a ranar Laraba jirgin ya taka nakiya, sannan aka buɗe masa wuta a daidai saitin da direba yake da kuma tankin jirgin”.

“Ina cikin jirgin da safiyar nan a lokacin da jirginmu ya bi ta kan nakiya ta tashi, Ikon Allah ne kawai ya sa muka tsira,” in ji tsohon sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya.

Labarai Makamanta