An ba tubabbun Boko Haram da aka mayar cikin al’umma tallafin naira dubu 20 da kayan sana’a sannan za a biya musu kudin haya.
A jiya ne aka yi bikin yaye tubabbun Boko Haram 601 da aka gama horas da su akan canja hali sannan kuma aka sake su cikin al’umma.
An baiwa kowannen su naira dubu 20 da kuma kayan sana’a sannan an ce su nemo shagunan da za su yi wadannan sana’o’i za a biya musu kudin haya.
Kwamishinan yada labarai na jihar Borno, Babakura Jatau ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace ba gaskiya bane labaran da ake yadawa cewa wai gwamnatin jihar ta baiwa kowane tubabben dan Boko Haram tallafin dubu 100.
Ya ce ma’aikatar kula da yankin NEDC da kuma wata kungiyar Agaji ce suka bayar da tallafin.
Ya kara da cewa kaso 10 cikin wanda aka yaye din ne Boko Haram na ainahi, sauran wanda suke ba su hadin kai ne ta hanyoyi daban-daban da kuma wanda aka kwato daga hannun kungiyar da ta yi garkuwa da su.
Ya ce za a kai tubabbun Boko Haram din Borno daga Gombe inda za a ajiye su a wani gida da aka tanada inda za su fara aiwatar da horon da aka ba su.
You must log in to post a comment.