Tsaro A Kaduna: El Rufa’i Da Uba Sani Sun Gana Da CAN

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El’rufai, da Sanatan Kaduna ta Arewa Uba Sani sun karbi bakuncin tawagar kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN), a karkashin jagorancin shugabanta na kasa Rebaren Samson Olasupo Ayokunle, a fadar mulkin Jihar, Kashim Ibrahim.

Rahotan ya bayyana cewar ziyarar da kusoshin kungiyar Kiristocin suka kai, yana daga cikin salon da Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumonin tsaro suke dauka na kawo karshen hare-haren da Yan taadda suke kai wa a wadan su daga cikin kananan hukumomi guda 5 na Jihar, kuma ziyarar CAN din wata manuniya ce dake nuni da cewar ta hanyar hadin kai ne kawai zamu iya yaki da Hare-Hare da Sanatar mutane da sace-sace da satar Shanu da sauran miyagun ayyuka.

Kazalika ziyarar zata temaka gaya wajen mayar da hankali wajen bakin tsare tare da magance matsalolin tsaron, dole sai mun yarda cewar mu Al’umma daya ne dole sai mun hada kai tare da son juna wanda hakan zai tabbatar da cikakken zaman lafiya da kaunar juna, kuma wannan shine lokacin daya kamata jagororin sun fito sun nunawa Al’umma muhimmancin zaman lafiya.

Rahotan ya bayyana cewar jawabin shugaban CAN yayi jawabi ne mai ratsa zuciya, kuma haka ya kamata ko wane Jagora ya zama.

Gwamnatin Jihar Kaduna, ta dukufa ai’nun wajen tabbatar zaman lafiya da tsaro a kudancin Jihar Kaduna da kwaryar Jihar, Gwamna El-Rufai, yana kan tsarin sa na kokarin tabbatar da zaman lafiya da kaunar juna a tsakani, kuma Gwamnatin sa zata yi dukkan mai yiwuwa don tabbatar da haka a Jihar.

Fata na ne cewa ziyarar ta shugabanin kungiyar ta kasa CAN za ta fara kulla jituwa tsakanin jama’ar Kudancin Kaduna da Gwamnatin Jiha domin a kulla kawance don kawo hadin gwiwa.

An tura Sojoji na musamman zuwa Kudancin Kadun, samun goyon bayan mutane yana da matukar muhimmanci ga manufa ta yi nasara.

Sanata Uba Sani, a nashi bangaren ya ce “Zan ci gaba da aiki tare da Gwamnatin Jiha da hukumomin tsaro don kawo karshen matsalar rashin tsaro a Kaduna ta Tsakiya.

Yace mutanen mu sun yi asara da yawa rayuwarsu, mu sani rayuwar su tana da mahimmanci a gare mu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply