Tsaftar Muhalli Ne Matakin Kariya Daga Cututtuka – Shugaban Karamar Hukumar Bauchi

Shugaban karamar hukumar Bauchi Mahmud Baba Ma’aji ya bayyana tsaftace muhalli a wani mataki na samun kariya daga daukan chututtuka masu saurin yaduwa a cikin al’umma,

Shugaban yayi wan nan bayani ne a lokacin da yake zagayawa cikin gari don gane ma idonsa yadda mutane ke ko-inkula da tsaftar muhallin na karshen wata a jihar Bauchi.

Kana ya kara da cewa, mutane ya kamata su baiwa hukuman tsaftace muhalli ta jihar goyon baya, domin ganin an cimma muradin kiwon lafiya na gwamnatin jihar da akasa a gaba.

Baba Ma’aji ya kara da cewa “Gudumuwar mu na farko zamu bayar da cikakken hadin kai ma hukumar tsaftace muhalli, da kuma wayar da kan al’umma muhimmanci ta bangaren tsaftace muhalli”

kana ya ce “bashakka muna da shirye shirye musamman a bangaren kiwon lafiya, mun sani idan babu kyakkyawar ingantaciyar muhalli, yana da wuya a samu lafiya mai dorewa, in muka zauna zamu bada fifiko ta wannan fanin”

A sharar da akeyi ko wani karshen wata, Shugaban hukumar tsaftace muhallin ta jihar Bauchi Dr. Kabir Ibrahim yace suna samun nasarori akan tsaftar muhallin, kana yace “shiyasa ma zamu fadada zuwa sauran kana nan hukumomin, in baku manta ba anyi korafi na karanci ma’aikatanmu a wasu wurare, to amma yanzu mun shawo kan matsalar.

Dr. Ibrahim yaci gaba da cewa “akwai anguwanni da suke bada tasu gudumuwar sosai ta wajen aikin gayya, amma masu amfani da ababen hawa abun sai a hankali, mutane basu son su zauna, su kula da muhallinsu sai kaga sun fito lokacin da akasa dokan yin sharar kuma bai kare ba, musamman manyan motoci akan manyanyan hanyoyi”

Daga karshe shugaban yayi kira ga al’umman ciki da wajen garin Bauchi dasu rika bin doka ko wace iri ce sau da kafa domin a zauna lafiya.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta

Leave a Reply