Tsadar Rayuwa: Kungiyar Kwadago Ta Bukaci Buhari Ya Kara Albashin Ma’aikata

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ƙungiyar kwadago ta ƙasa NLC ta nemi gwamnatin Tarayya ta kara albashin ma’aikata da kashi 50 cikin 100 lura da yanayin tsadar rayuwa.

NLC ta mika wannan bukata ga shugaba Muhammadu Buhari ta wasikar da ke dauke da sa hannun shugabanta Ayuba Wabba.

Wasikar ta yi tuni da cewa gwamnonin su suka karfafa batun janye tallafin mai, da kawo batun ritayan ma’aikatan gwamnati a shekara 50, da kuma rage kudaden da ake bai wa majaliasa domin aikin mazabu.

Ƙungiyar ta caccaki gwamnoni kan wadannan shawarwari, su na mai cewa duk wanda ya goyi bayan ra’ayinsu to ba shi da maraba da makiyin gwamnati.

NLC ta ce batun karin albashi ne abin da ya kamata a mayar da hankali a kai, domin a wannan lokaci shi ne mai muhimmanci.

Masu fafutikar dai na ganin akwai bukatar gwamnati take amfani da yanayin kasa da abubuwan da ke faruwa wajen fayyace albashi da samawa ‘yan kasar sauki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply