Titin Dogon Kano Zuwa Maradi: Majalisa Ta Soki Amaechi

Kwamitin Haɗakar Sanatoci da Majalisar Tarayya masu lura da Sufurin Jiragen Ruwa da Jiragen Ƙasa, sun ragargaji Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, dangane da abin da suka kira fifita Jamhuriyar Nijar a kan wasu sassan Najeriya.

Amaechi ya sha ragargazar ce a ranar Alhamis, lokacin da ya bayyana a gaban Kwamiti domin kare kasafin 2022 na ma’aikatar sa.

Tun da farko dai an fara tankiya ce a kan dalilin da ya sa za a gina titin Jibiya zuwa Maraɗi na zamani, alhali kuma wanda za a gina daga Fatakwal zuwa Maiduguri ba na zamani ba.

Wato daga Jibiya zuwa Maraɗi za a gina ‘Standard Gauge’, amma daga Fatakwal zuwa Maiduguri kuma za a gina ‘Narrow Gauge’.

Shugaban Kwamitin Sufuri na Majalisar Tarayya, Pat Asada ne ya fara ragargazar Minista Amaechi, inda ya bayyana cewa akwai rashin bada muhimmanci ga wasu ɓangarorin ƙasar nan a ƙoƙarin Amaechi na daɗaɗa wa al’ummar Jamhuriyar Nijar.

“Don me za ka yi ta giringiɗishin neman bashin gina titin jirgi mai nisan kilomita 284 daga Kano zuwa Nijar, alhali kuma ga wasu sassan ƙasar nan, su na buƙatar titinan?

“Ka dubi irin harkokin kasuwancin da ake yi a yankin Kudu maso Gabas, ai su ne su ka fi buƙatar jiragen ƙasa ba Maraɗi ba.

“Maraɗi ba ta kai muhimmancin Kudu maso Gabas ga tattalin arzikin ƙasar nan ba. Ballantana kuma yankin Kudu maso Kudu.”

Shi kuma Sanata Ɗanjuma Goje, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Sufurin Jiragen Ruwa, ya yi ƙorafin cewa, “a gaskiya kuɗaɗen da ake kashewa wajen aikin titin jirgi daga Lagos zuwa Ibadan, sun yi yawa, kuma sun wace hankalin mai tunani.

Sannan kuma Goje ya tambayi Amaechi cewa, “shin laifin me muka yi maka a Kudu maso Gabas, Benuwai, Filato, Taraba, Bauchi, Gombe, Barno da Adamawa da ba za a yi mana titinan jirgin ƙasa ba? Ko mu ba ‘yan Najeriya ba ne?”

Da ya ke maida jawabi, Amaechi ya ce ai babu wani bambanci tsakanin titunan jiragen. Na Maraɗi da aka ce ‘standard gauge’ ne, ai iyakar tsawon wannan titin kilomita 20 ne kacal daga Jibiya zuwa Maraɗi.

Babu Kuɗin Aikin Titin Jirgin Kasa Da Ibadan Zuwa Kano -Amaechi:

Minista Amaechi ya taɓo batun ƙarancin kuɗaɗe, ya shaida masu cewa yanzu haka babu kuɗin da za a yi aikin titin jirgin ƙasa daga Ibadan zuwa Kano.

“Saboda babu kuɗin da za a yi aikin, sai an ciwo bashi. Saboda babu kuɗin shi ya sa gwamantin tarayya ta taƙarƙara za ta gina daga Kano zuwa Ibadan da kudin ta, kafin a samu bashin.”

Ya ƙara da cewa shi ma aikin gina titin Fatakwal zuwa Maiduguri duk babu ko sisi a ƙasa, sai an ciwo bashi za a yi aikin tukunna.

Labarai Makamanta