Tinubu Zai Jagoranci Laccar Gidan Tarihin Arewa Yau Asabar

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai shugabanci laccar da za’a gudanar a cibiyar Arewa karo na 11 a ranar yau Asabar.

Daraktan gidan tarihin Arewa Dr Shuaibu Shehu Aliyu ya bayyana hakan ga manema labarai aKaduna ranar Alhamis.

Yace laccar karshe wato ta 10, wadda gwamnan babban bankin Najeriya na wancan lokacin, Sanusi Lamido Sanusi, ya gabatar kuma Oba na Lagos Oba Rilwan Akiolu ya shugabanta.

A yanda yace, An lura sosai wajen zabar Tinubu da Lalong domin jagorantar laccar.

“Ina mai farin cikin sanar daku cewa gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong zai gudanar da laccar wannan shekarar a karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar 27 ga watan Maris na 2021.”

Laccar wacce aka shirya ta musamman domin wayar da kai kan hadin kan kasa. An zabi gwamna Lalong ne duba da cewa shine shugaban gwamnonin Arewa da kuma kwarewar sa wajen jagorantar jihar Filato.

Ana ma gwamnan kallon ya zaiyi da rikice-rikicen jihar na tsawon shekaru 20 baya. Amma daga hawan sa mulki ya samu ya kawo karshen wadannan rikice-rikicen.

“Haka kuma dangane da shugabanci, a koda yaushe muna duba ayyukan da muhimman mutane sukayi kafin mu zabi wanda zai shugabanci laccar.

Asiwaju Bola Tinubu an zabe shi domin ya kara ma taron armashi da kuma kawo cigaba da hadin kan kasa” inji Daraktan.

Ya bayyana cewa laccar shekara-shekara ta cibiyar Arewa wato ‘Arewa House’ ta kasance ana gudanar da ita tun shekarar 1994.

Kuma laccar ta kunshi kowa da kowa ba tare da duba da kabila, addini ko kuma siyasa ba. A na dai gabatar da laccar ne domin girmama tsohon Firimiyan Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

Gwamna Lalong zai yi magana ne akan ‘yadda za’a rage yawan kashe kuɗi a gwamnati da kuma sanya matasa wajen kawo cigaban kasa bayan annobar Korona.

Labarai Makamanta