Tinubu Ya Samu Gagarumar Tarba A Jihar Kano

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Laraba a jihar Kano, ya bayyana fatansa na ganin jam’iyyarsa za ta lashe jihar Kano da Najeriya baki daya, a zaben 2023.

Tinubu, wanda al’ummar jihar suka yi masa gagarumin tarba, ya je Kano ne domin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na Arewa maso Yamma.

Ya godewa al’ummar jihar bisa gagarumin fitowar da suka nuna, goyon baya da hadin kai.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su zabi APC tun daga sama har kasa a zabe mai zuwa.

Ya kuma tabbatar wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC cewa kuri’un mutanen Kano na APC ne, inda ya ce jama’a sun ga ribar dimokuradiyya da gwamnatin APC ta samar.

Gwamnan ya ce jam’iyyar ta amince kuma ta samu kwarin guiwar dimbin jama’a da suka tarbi Asiwaju Bola Tinubu a Kano.

“Nasarar da aka samu taron bayyananne ne da kuma nuna fifikon mutanen Kano dangane da zabin da ke gabansu.

“Goyon bayan Gawun/Garo kuri’ar amincewa ce ga dan takarar gwamna da mataimakinsa,” NAN ta ruwaito na cewa.

Ganduje ya ce Tinubu yana da hali, iya aiki da kuma cancantar samar da shugabanci da kowa zai yi alfahari da shi a kasar nan.

Labarai Makamanta