Labarin dake shigo mana daga birnin Ikko na jihar Legas na bayyana cewar Dan takara a zaben neman kujerar shugaban kasar Najeriya karkashin jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya sake baranbarama a wajen kamfe.
Yayin jawabi da gangamin mabiya dake wajen taro a filin kwallon Teslim Balogun, tsohon gwamnan na Legas yace su je su karbi katin “APV”. Yayinda yake kokarin gyarawa kuma ya sake tafka wata baranbaramar yace APC.
Yace: “Shin kuna so na? Ku je ku karbi APV…APC kuma wajibi ne kuyi zabe.” Ba yau farau ba Dan takaran na APC ya kwan biyu yana subul-da-baka yayin jawabi ga jama’a a kwanakin nan.
A lokacin taron kamfen farko da APC ta gudanar a garin Jos, jihar Plateau, Tinubu ya yiwa jam’iyyar PDP addu’a maimakon APC. A jihar Kaduna kuwa yayin kokarin jinjinawa El-Rufa’i, ya sokesa. Yace: “El-Rufa’i ya mayar da rubabben lamari lalatacce.”
Shi yasa wasu suka yi zargin kin halartan taron muhawarar ARISE TV da Tinubu yayi, yana tsoron magana ne saboda bai da isasshen lafiya.
‘Yan Najeriya da dama na zargin cewa Tinubu bai da isasshen lafiya kuma bai cancanci yin shugabancin Najeriya ba.
You must log in to post a comment.