Tinubu Ya Roki Buhari Ya Dauki Matasa Miliyan 50 Aikin Soja

Jagoran jam’iyya mai mulkin ƙasar nan (APC) Bola Tinubu,ya kirayi gwamnatin tarayya da ta ɗauki matasa miliyan 50 aikin soja don magance matsalar tsaro data addabi ƙasar.

A jawabin da ya yi a wajen taron bikin murnar cikarsa shekaru 69 a duniya, Tinubu yace ɗaukar wannan matakin zai kara taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci.

“Muna ƙarkashin ‘yan sanda kuma muna fama da matsalar ‘yan fashi da makami, da ‘yan bindiga. A ɗauki matasa masu ɗanyen jini a jiki aikin soja kamar mutum miliyan 50 domin shawo kan matsalar.

“Ku daina cewa jahilci ke damun su, duk mutumin da zai iya riƙe bindiga, zai iya sarrafa ta, kuma zai iya shiryawa ya yi harbi da ita to wannan zai iya gyara babbar mota a gareji.”

Tsohon gwamnan jihar Lagos ɗin ya jinjina ma matasa musamman waɗanda suke nuna a shirye suke wajen taimakawa a dawo da zaman lafiya a ƙasar nan.

Taron wanda ya gudana a jihar Kano anyi masa take da: “Hadin kan mu, arzikin mu: Wajibi ne ga hadin kan kasa don girma da ci gaba”.

Labarai Makamanta