Tinubu Ya Fusata Da Yawaitar Kashe-Kashe A Najeriya

Sakamakon ci gaba da kashe-kashe da sace-sacen ‘yan kasa da ake zargin‘ yan bindiga da ‘yan fashin daji suna yi a fadin kasar nan jigo a jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya mayar da martani da kakkausar murya.

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, @AsiwajuTinubu, a ranar Alhamis, 29 ga Afrilu, babban jigon na APC ya ce ya damu da ta’addanci da zaluncin da ake kai wa mutane musamman a jihohin Borno, Yobe, Benuwai, Neja, da Imo.

Ya bayyana cewa hare-haren sun sa jama’a da dama sun shiga mawuyacin hali tare da yanke ƙauna ta samun kariya daga soji da sauran jami’an tsaron kasar.

Tsohon gwamnan na Legas, ya bayyana cewa dole ne gwamnati ta ci gaba da karfafa wa jami’an tsaro gwiwa don yin iya kokarinsu don shawo kan wannan barazanar.

Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kar su taba mika wuya ga jaraba na zargin juna duk da banbancin yanki ko addini. Yayinda yake lura da cewa dole ne kowa ya hadu wajen yakar abokin gaba daya, tsohon gwamnan ya ce rashin jituwa zai kawo rashin nasara ne kawai.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Labarai Makamanta