Tilasta Bin Doka Ne Aikina Ba Wa’azi Ga ‘Yan Bindiga Ba – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sake jaddada rantsuwa da cewa ko kaɗan gwamnatinsa ba za ta tattauna da ‘yan bindiga da masu aikata laifi ba, domin babu dalilin yin hakan ta kowane ɓangaren.

El Rufa’i ya ƙara da cewar aikinsa a matsayin Gwamna shi ne tilasta doka da gurfanar da masu laifi amma ba da’awar tuba da lallami a gare su ba.

El-Rufai ya maimaita matsayin gwamnatinsa yayin fadada taron majalisar tsaron jihar a zauren majalisar na gidan Sir Kashim Ibrahim a ranar Talata.

Baya ga mambobi na yau da kullum daga gwamnatin jihar, hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya, taron ya hada da shugabannin addinai da kuma baƙin da aka gayyata daga kungiyoyin kwararru, ƙwadago da na fararen hula.

“Ba za mu yi hulda da ‘yan bindiga ko masu satar mutane ba. ‘Yan kasa masu zaman kansu kamar malamai na iya yin hakan a cikin ikon su, don yi musu wa’azi da rokon su tuba.

Muna kuma son su tuba amma ba aikinmu bane mu nemi su yi hakan,” ya jaddada. A cewarsa, hanya mafi kyau ta magance rikice-rikicen manoma da makiyaya, satar shanu da fashi da makami shi ne makiyaya su yi rayuwa ta zama waje daya don su zama masu amfani kuma su bai wa yaransu ilimi da kuma samun ingantaccen kiwon lafiya.

Gwamnan ya bayar da hujjar cewa, an daina kiwo irin na da ko kuma kiwon shanu a fili saboda bunkasar birane da karuwar jama’a domin yawancin hanyoyin da shanun ke bi sun zama garuruwa.

El-Rufai ya ce Gwamnatin jihar Kaduna na aiwatar da wani babban aiki na kiwo a Filin Kiwo dake Damau a karamar hukumar Kubau, ya kara da cewa aikin zai tallafawa makiyaya kusan 1,500. Ya jaddada cewa aikin zai baiwa makiyaya damar kiwon shanunsu a wani wuri da ya kunshi wuraren kiwo, makaranta da Cibiyar Kiwon Lafiya ta matakin Farko tare da samar da abokan kasuwanci da ke shirye don siyan madarar shanu.

Labarai Makamanta