Tattalin Arzikin Najeriya Zai Yi Farfadowar Ban Mamaki – Ministan Sadarwa

Labarin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, yace bada jimawa tattalin arzikin Najeriya zai yi wata irin farfaɗowa ta ban mamaki ya shiga sahu mafi karfi a duniya.

Ministan ya yi wannan furucin ne a wurin taro karo na biyu a tsangayar kimiyya da fasaha ta kwalejin fasaha dake Bauchi. Pantami yace taken taron, ‘Rawar kimiyya da fasaha da kirkire-kirekire a tattalin arzikin zamani: Domim kawo cigaba mai ɗorewa’ ya na da alaƙa da manufar tattalin arzikin zamani.

“Yana da matukar amfani saboda kasar mu Najeriya takai wani mataki na shiga jerin kasashen nan da yan wasu shekaru masu zuwa za’ai gogayya da su ɓangaren karfin tattalin arzikin zamani.” “Wannan shine fata da burin ma’aikatar sadarwa da kuma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kuma duk wata hukuma dake karkashin ma’aikatar sadarwa, masu zaman kansu, su maida hankali kan tattalin arzikin zamani.”

“Kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire sune hanyoyin gano wasu ko ba duka ba hanyar kawo karshen yunwa ta hanyar zamanantar da noma, fita daga talauci, samun kyakkyawan lafiya da sauransu.

Pantami wanda ya samu wakilcin daraktan kamfanin Galaxy Backbone Plc, Muhammad Abubakar, a wurin taron. Bugu da kari ministan ya kara da bayyana cewa tattalin arzikin zamani na Najeriya ya fara ɗauƙan kyakkyawar hanyar haɓaka.

Yace hakan ya haifar da sakamako mai kyau, ta yadda kasuwanci yake bunkasa cikin tsari mai kyau, da yadda mutane ke biyan bukatunsu na bayanai da kayayyakin amfani.

Labarai Makamanta