Tattalin Arzikin Najeriya Zai Bunkasa A Shekarar 2023 – Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana sa ran tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi uku cikin 100 a shekarar 2023.

A wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar kan yanayin bunƙasar tattalin arzikin duniya a shekarar 2023, ta ce ƙaruwar hauhawar farashi da ƙarancin wutar lantarki na yin tasiri a kan haɓakar tattalin arzikin Najeriya.

”To sai dai tattalin arzikin zai bunƙasa ta hanyar haɓakar kasuwanci da sauran sana’o’i, lamarin da zai sa bunƙasar ta kai kashi uku cikin 100.”, in ji rahoton.

Rahoton ya ƙara da cewa ana sa ran samun haɓakar tattalin arziki ne a gabashi da yammacin Afirka.

Haka kuma rahoton ya yi hasashen cewar ƙaruwar farashin kayayyaki zai taimaka wa masu safarar kayayyakin, to sai dai kuma ta yi gargaɗin cewar ruguwar ɓukatar kayayyakin a duniya ka iya haifar da kalubale.

Labarai Makamanta