Tattalin Arzikin Najeriya Ya Yi Habakar Da Ba A Taba Gani Ba – Buhari


Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mai girma Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tattalin Arzikin Kasar na habakar da ba a taba ganin irinta ba, tun bayan karbar mulkinsa.

An ruwaito mai magana da yawun Shugaban kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya bayyana hakan a cikin wata takardar sanarwa da ya fitar kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja.

Inda ya ce, a yanzu tattalin Arzikin ya samu tagomashin karin kaso 5.01% a tsakiyar wannan shekara, wanda idan aka kwatanta da shekarun baya za’a gane cewar haɓakar arzikin Najeriya ya yi matukar habaka da cigaba.

Tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 5.01 a tsakanin watan Afirilu zuwa watan Yuni na 2021 daga kashi 0.51 da aka samu a watanni uku na farkon shekarar nan.

Rahoton daukacin kayan aiki da kasar nan ta samar a na watanni uku wanda NBS ta fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa wannan cigaban na kashi 5.01% shine mafi girma da aka taba samu tun daga karshen shekarar 2014. Wannan habakar tattalin arzikin ya fi na wancan shekarar 2020 da ta gabata tare da ta watanni uku na farko na wannan shekarar da aka gani.

Rahoton ya ce wannan alamu ne na dawowar kasuwanci da al’amuran tattalin arziki bayan aukuwar muguwar annobar korona. NBS ta kara da bayanin cewa: Farfadowar tattalin arzikin kasar nan da ya fara daga karshen 2020, tare da dawowar al’amuran kasuwanci a gida Najeriya da duniya baki daya, shine silar cigaban da ake gani.

Kiyasi kan rahoton ya nuna cewa bangaren da ba na man fetur ba ya samar da kashi 6.74 inda sauran kashin an samo shi ne daga kasuwanci, yada labarai da sadarwa, sufuri da sauransu kamar yadda rahoton ya sanar.

To sai dai ikirarin shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da talakawan kasar ke dandana kudarsu ta fannin hauhawar farashin kayan masarufi, musamman ma kayan abinci wadanda farashinsu ya yi tashin gwauran zabi a kasuwannin Kasar.

Labarai Makamanta