Tattalin Arzikin Najeriya Ya Sake Farfadowa

Rahotonni daga Hukumar ƙididdiga ta ƙasa na bayyana cewar tattalin arzikin Najeriya ya karu da kashi 0.11 bisa dari a zango na hudu na shekarar 2020, wanda ke wakiltar ci gaban farko a cikin zango uku da suka gabata.

Rahoton ya cigaba da cewar “Koda yake yana da rauni, ci gaban da aka samu yana nuna yadda ayyukan tattalin arziki ke dawowa sannu a hankali biyo bayan cire dokar takaita zirga-zirga da kuma takaita ayyukan kasuwanci na cikin gida da waje a zangon da suka gabata.

“A sakamakon haka, yayin da bunkasar Q4 2020 ya yi kasa da na bunkasar da aka samu a shekarar da ta gabata da kashi –2.44, ya karu da kaso 3.74 idan aka kwatanta da Q3 2020.

“A abinda akan samu kwata bayan kwata, ainihin bunkasar GDP ya karu da kashi 9.68 cikin dari wanda ke nuna ci gaba a karo na biyu a jere na ainahin bunkasar da aka samu a cikin shekarar 2020 bayan akasin da aka samu a zango biyu.

“Gaba ɗaya, a cikin shekarar 2020, an kiyasta ci gaban da aka samu a GDP na shekara-shekara da -1.92 bisa ɗari, raguwar kashi -4.20 idan aka kwatanta da kashi 2.27 da aka samu a shekarar 2019.”

An samu kimanin gangar mai miliyan 1.56 a kowace rana a cikin zango huɗu na 2020; 0.11 ƙasa da abunda aka samu a zango na uku, kamar yadda rahoton hukumar ya bayyana.

A kan shekara-shekara, bangaren mai ya bunkasa zuwa -19.76 bisa dari. Bangaren mai ya ba da kashi 5.87 bisa ɗari na jimlar GDP a Q4 2020.

Wannan rahoton da Hukumar ƙididdigar ta fitar na matsayin wani abin cigaba ne ga ɓangaren tattalin arzikin kasar wanda ya daɗe yana fuskantar kalubale tun bayan hawa karagar mulki ta Shugaban ƙasa Buhari.

Labarai Makamanta