Tashoshin Jiragen Ruwa: An Kori Hadiza An Tabbatar Da Koko

Shugaba Buhari ya amince da Korar Hadiza Bala Usman kuma da nadin Mohammed Bello Koko a matsayin shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA

Ma’aikatar sufuri ta sanar da hakan a ranar Talata ta wata takarda wacce darektan yada labaran ma’aikatar, Eric Ojiekwe ya sa hannu Kafin a nada shi,

Koko ne darektan sha’anonin kudi da gudanarwa na hukumar NPA din, kamar yadda takardar ta bayyana

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mohammed Bello Koko a matsayin shugaban hukumar kula da tashohin jiragen ruwa, NPA, mai cikaken iko,

The Cable ta ruwaito. Mai magana da yawun ma’aikatar sufuri na tarayya, Eric Ojiekwe, ne ya sanar da hakan cikin wata takarda da ya fitar a ranar Talata.

Kafin nadinsa, Koko ne babban direktan sashin kudi da gudanar da mulki a NPA kamar yadda
sanarwar ta ce.

Ofishinta Koko zai maye gurbin Hadiza Bala Usman, wacce aka dakatar a watan Mayun 2021 bisa zargin batar da Naira miliyan 165 kuma a kora a ranar talatannan

An dakatar da Usman ne bayan ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya hada wani kwamiti wanda zai yi bincike akan yadda ake gudanar da ayyukan NPA. Bayan dakatar da ita, Buhari ya nada Koko a matsayin shugaban NPA na wucin-gadi kafin a kammala binciken.

An zargi Usman da wawusar Naira biliyan 165, zargin da ta musanta A shekarar da ta gabata, The Cable ta ruwaito yadda ministan ya zargi hukumar, karkashin shugabancin Usman da rashin shigar da rarar kudi ta Naira biliyan 165.

Labarai Makamanta