Taraba: Zaben Kungiyar ‘Yan Dako Ya Bar Baya Da Kura

Labarin dake shigo mana daga Jihar Taraba na bayyana cewar Mutane bakwai ne suka jikkata bayan wani sabani da ya afku kan zaben shugabannin kungiyar ‘yan dako a kauyen Sabongida da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba a ranar Laraba.

An ruwaito cewa rikicin ya fara ne a karshen makon da ya gabata bayan kungiyar ta gudanar da zabe domin samar da sabbin shugabanninta na shekaru biyu masu zuwa.

Wani shaidan gani da ido Nuhu Sabongida, ya ce an gudanar da zaben cikin lumana kuma mutane da dama sun yarda cewar an yi shi cikin gaskiya da amana.

Mallam Murtala Muhammed ne ya zama sabon shugaban tare da sauran jami’ai 11 bayan ya kayar da shugaba mai ci, Yakubu Saleh inji shi.

Bayan kayen da ya sha, sai tsohon shugaban Saleh ya je wajen shugaban karamar hukumar, Alhaji Musa Abdullahi Chul, don yin zanga-zanga.

An tattaro cewa a ranar Talata shugaban karamar hukumar ya umurci shugaban yan sandan Gassol da wasu jami’an kungiyar da su raka Saleh sannan su nada shi ya ci gaba a matsayin shugaban kungiyar.

“A kokarin tursasa tsohon shugaban kan kungiyar ne rikici ya fara tsakanin kungiyoyin hamayya.” Wata majiya ta ci gaba da cewa, an samu tashin hankali a kauyen Sabongida a ranar Talata biyo bayan takun-saka tsakanin kungiyoyin biyu, wanda ya yi sanadiyar jikkata mutane bakwai.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Shugaban Kungiyar cigaban Sabongida, Alhaji Isiaka Adamu ya dora alhakin rikicin a kan shugaban karamar hukumar Gasol kan kokarin da ya yi na tursasa tsohon shugaban.

Shugaban karamar hukumar na so tsohon shugaban ya ci gaba saboda ra’ayin siyasarsa amma mutanen basa son sa kuma cewa wannan ne yasa suka zabi Abubakar. “Kamar yadda kuke gani, akwai fargaba lokacin da mutane suka ki cewa ya ci gaba da shirin rantsar da tsohon shugaban da aka kayar a zaben.”

Shugaban kungiyar ci gaban sabon gidan ya kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su saita shugaban Gasol domin guje ma ci gaba da karya doka da oda a yankin.

Da aka tuntube shi, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan Taraba, DSP Abdullahi Usman ya ce bai riga ya samu jawabi daga hedkwatar rundunar da ke Gasol ba. “Zan yi karin bayani da zarar mun samu cikakkun bayanai daga Gassol.”

Da yake martani kan zargin, shugaban karamar hukumar Gassol, Alhaji Musa Abdullahi Chul ya musanta tursasa wani dan takara a kan kungiyar. A cewarsa, Saleh Abubakar ya rubutawa karamar hukumar wasika inda ya sanar da majalisar cewa za su gudanar da zabensu inda aka tura jami’an hukumar kwadago don sanya ido kan zaben, inda ya kara da cewa an zabi shugaban da kuri’u mafi rinjaye.

Chul ya ce: “Zaben ya kasance bisa yarjejeniyar da suka yi kuma tun da mafi rinjaye sun zabi Saleh Abubakar sai muka yi aiki da hakan kuma muka rantsar da shi.”

Labarai Makamanta