TARABA: ‘Yan Fansho Sun Koka Kan Rashin Biya Sama Da Shekaru 10

BASHIR ADAMU, JALINGO.

Kungiyar Yan Fansho a Jihar Taraba, dake yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya, wato ‘Taraba State Concern Retirees’ tace daga gobe Labaraba, 18 ga Watan Junairun wannan Shekaran in Allah Ya kaimu zasu sake gudanar da wani zanga-zangar lumana kan rashin biyan tsoffin Ma’aikatan Gwamnatin Jihar dana Kananan Hukumomi Garatuti na tsawon shekaru goma sha- daya da kuma kin sanya sunayen tsoffin Ma’aikatan Kananan Hukumomin da suka ajiye aiki tun shekaru goma (10) da suka wuce izuwa yau a Kundin Rigistan tsoffin Ma’aikatan Gwamnati domin soma biyansu nasu Gratutin.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da Kungiyar ‘Taraba State Concern Retirees’ din ta fitar da ta aikewa Gwamnan Jihar Taraba, Darius Dickson Ishiaku a Jalingo dake dauke da sa hannun Shugaban Kungiyar, Komarade Silas Jefta da Sakataren shi, Komarade Pastor Yohanna-Ajiya da aka rabawa manema Labarai, Hukumar Kare Hakkin Dan’adam, Majalisar Jihar Taraba, Kungiyar Kwadago da dukkanin Hukumomin Tsaron Gwamnati dake fadan Jihar.

Bayanin dake kunshe a cikin takardan ya cigaba da cewa, a Shekaran daya gabata na 2022 sun aike da wasiku guda uku ga Gwamnan Jihar ta hannun Sakataren Gwamnatin Jiha, Kakakin Majalisar Jiha da Mataimakin Gwamnan Jihar da a biyasu hakkokinsu. Amma abun kunya da takaici, Gwamnan Jihar yaki daukan wani mataki don sheremusu jawayensu.

Adon haka, Yan- Fanshon suka dauki matakin gudanar da zanga-zangar lumana a gobe Labaraba 18 ga Watan junairun shekara na 2023.

Labarai Makamanta