TARABA: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Iyalai 8 Na Basarake A Jalingo

BASHIR ADAMU, JALINGO

Rahotannin dake zuwa mana yanzu daga Jalingo, fadan Gwamnatin Jihar Taraba, Arewa Maso Gabas, na cewa Yanbindiga dake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sunyi awon gaba da Mataye biyu da Yara shida na Sarkin Mutum Biyu, dake Karamar Hukumar Gassol, Mai-shari’a Sani Muhammad (Ritaya), a cikin Gidanshi dake Birnin Jaingo.

Mai- Martaba Sani Muhammad dai Sarki ne mai daraja ta biyu a Jihar.

Rundunar Yansandan Jihar Taraba, a Ranar Juma’ah ta tabbatar da aukuwan mummunan lamarin ga manema labarai a Jalingo a tabakin mai magana da yawun Rundunar Yansandan Jihar, SP. Abdullahi Usman

Abdullahi yace wadanda ake zargin da mummunan aika- aikan sun dira cikin gidan basaraken ne a Jalingo cikin tsakiyar daren ranar Alhamis inda sukayi awon gaba da matayen Sarkin biyu tare da yaranshi guda shida.

Abdullahi ya kara da cewa daga samun rahoton aukuwan lamarin, Rundunar Yansandan ta baza jami’anta domin tabbatar da kubutar da Iyalan basaraken da akayi garkuwa dasu cikin koshin lafiya.

Wasu bayanai da Wakilinmu ya tattara, sun tabbatar da cewa Basaraken baya cikin gidanshi na Jalingon sa’ilin da Masu garkuwa da mutanen suka shiga.

Labarai Makamanta