Taraba: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Sojoji

Rahotanni daga Jalingo babban birnin jihar Taraba na bayyana cewar Yan bindiga sun kashe sojoji shida yayin da suke hanyar su ta zuwa wurin da aka kai hari a Tati, wani ƙauye da ke karamar hukumar Takum, a cewar rundunar Sojojin Najeriya cikin wani sako na cikin gida da ta fitar.

A cewar takardar da rundunar sojojin ta bataliya 93 da ke Takum ta aike, kawo yanzu ba a gano inda kwamandan bataliyar, E.S. Okore, mai muƙamin laftanar kanal ya ke ba.

Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar 10 ga watan Mayu, ‘yan bindigan sun fi sojojin yawa sosai. Takardar ta kuma ce ba za a iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu a bangaren ‘yan bindigan ba.

Takardar ta ce har yanzu sojoji na aikin bincike da ceto a yankin. Jihar Taraba dai na samun karuwar laifuka da garkuwa da mutane musamman a Jalingo, babban birnin Jihar.

Labarai Makamanta