Taraba: Shanu Da Dama Sun Mutu Sanadiyyar Ruwan Bama-Baman Soji

Labarin dake shigo mana daga Jihar Taraba na bayyana cewar kimanin shanu 1500 ne aka rasa sakamakon luguden ruwan wutar da sojojin sama suka yi a wata rugar Fulani da ke karamar hukumar Takum dake Jihar.

An ruwaito cewa, jiragen yakin sun kaddamar da luguden wutan kan gidajen Fulani makiyaya da ke wurin Kashinbila da Tor Donga a ranakun Laraba da Alhamis inda suka kashe shanu 1500, sun saki ruwan wutan ne wurin karfe 11 na safe da kuma hudu na yammacin Laraba da Alhamis.

Wani wanda lamarin ya shafa mai suna Sadu Saidu, ya sanar da cewa ya rasa kusan shanu guda dari da ashirin yayin da dan uwansa ya rasa shanu dari da biyar. “Za mu jagoranci shanunmu zuwa wurin kiwo kenan lokacin da muka ji karar jirgi kuma suka fara barin wuta.

Mun tsere tare da tsayawa karkashin manyan itace kuma a take suka kashe mana shanu dari bakwai,” Sadu yace. Ya ce wannan jirgin ne ya sake dawowa a rana ta biyu inda ya kai farmakin ruga biyu tare da kashe shanu kusan dari bakwai da hamsin.

Wani wanda abun ya shafa mai suna Musa, ya ce baya da kashe shanun, da yawa daga cikin shanunsu sun raunata kuma sun watsar da su a garin Takum. Ya ce lamarin ya sa daruruwan Fulani sun kada shanunsu zuwa Kamaru.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, Usman Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar al’amarin amma ya ce a jihar Binuwai ne lamarin ya faru ba a Taraba ba.

Labarai Makamanta