Taraba: PDP Ta Yi Tuwona Maina A Zaben Fidda Gwani

BASHIR ADAMU, JALINGO

Rahotannin dake zuwa mana daga Jihar Taraba na cewa anyi tuwona maina a zabubbukan fidda gwani na ‘yan-takaran da za su wakilci Jam’iyyar PDP a zaben shekara 2023.

Inda Shugaban Jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Taraba, Laftanal Kanar, Agbu Kefas, mai Ritaya, wanda tun a farko ake zargi da cewa shine dan-takaran da jigo a Jihar ta Taraba, Janar T.Y. Danjuma mai Ritaya, ya kakaba musu duk da cewa Jam’iyyar Jihar basu aminta da dan takaran ba, ya lashe zaben fidda gwani na Gwamna da kuri’u 443, cikin ingantattaun kuri’u 517 da masu zabe/’delegates’ suka kada, inda Kakakin Majalisar Jihar, Rt. Hon. Joseph Albasu Kunini yazo na biyu da kuri’u 31.


Zaben ya gudana ne a Fillin Wasanni na Jolly Nyame dake Jalingo.

Shi kuma Gomnan Jihar Taraba, Arch. Darius Dickson Ishiaku ya sami nasaran zama dan takaran Sanata da babu hamayya, a shiyyar Taraba ta Kudu da dukkanin ingantattun kuri’u 154 da’aka kada masa.
Zaben ya gudanane a Karamar Hukumar Wukari dake Jihar Taraba.

Inda shima Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Engnr. Haruna Manu ya sami nasaran zama dan-takaran Sanata a shiyyar Taraba ta tsakiya da kuri’u 143, inda Muhammed Abana yazo na biyu da bai sami kuri’a ko daya ba.


Zaben ya guda ne a Karamar Hukumar Bali dake Jihar Taraba.

Shima, Shugaban Marasu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Shu’aibu Isa Lau ya sami nasaran zama dan-takaran Sanata a shiyyar Taraba ta Arewa da kuri’u 193, inda David Kasa ke bi masa da kuri’u 73.
Zaben ya gudana ne a Fillin Wasanni na Jolly Nyame dake Jalingo.

Abin jira a gani anan shine, wai shin wadannan yan- takaran na Jam’iyyar PDP zasu sami nasara a zabubbukan gama-gari na shekara ta 2023 da zai gudana indan Allah Ya kaimu, lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan.

Labarai Makamanta