Taraba: Masarautar Muri Ta Ba Makiyaya Wa’adin Wata Guda Su Bar Yankin

Rahotanni daga Jihar Taraba na bayyana cewar Sarkin masarautar Muri a jihar, Abbas Tafida ya ba da wa’adin kwanaki 30 ga makiyaya da ke addabar mazauna yankin kan su bar dazuzzukan fadin masarautar ko kuma a tilasta musu yin hakan.

Rahotanni sun bayyana cewa Sarkin ya bayar da wa’adin ne a ranar Talata bayan sallar Idi. Wannan ya biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane, kashe-kashe, da hare-hare a jihar da wasu miyagu da ake zargin makiyaya ne ke aikatawa.

Basaraken Ya yi ikirarin cewa Fulani makiyaya ne ke da alhakin aikata laifuka a jihar don haka ya kamata su bar dazuzzukan da ke cikin jihar cikin kwanaki 30 ko kuma a tilasta musu fita.

Sarkin ya bukaci shugabannin Fulani Makiyaya da su fitar da bara-gurbi a tsakanin su, cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

“Fulaninmu makiyaya a dazuzzuka, kun shigo wannan jihar ne kuma mun karbe ku, me ya sa za ku zo garuruwa da kauyuka don satar mutane, har ma da fyade ga matanmu?

“Saboda wannan barazanar da ta ki karewa, an ba kowane Bafulatani makiyayi a wannan jihar kwanaki talatin ya bar cikin dazuzzuka. “Mun gaji da rashin bacci ba dare ba rana, kuma yunwa kadai a cikin kasar nan na da girman da ba za mu bari ta ci gaba ba.”

Jihar Taraba da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na fuskantar munanan ayyukan ta’addanci kama daga satar mutane zuwa hare-haren ‘yan bindiga.

Labarai Makamanta