Taraba: Kotu Ta Tabbatar Da Sanata Bwacha Matsayin Dan Takarar Gwamna Na APC

BASHIR ADAMU, JALINGO

Kotun daukaka kara ta Gwamnatin Tarayya da ke zamanta a Yola, a ranar Alhamis ta yi watsi da hukuncin da babbar kotu ta yanke a baya na soke zaben fidda gwanin da ya gabatar da Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Taraba

Kotun ta kuma bayar da umarnin a mika sunan Sanata Bwacha ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a matsayin sahihin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Taraba.

A nashi bangaren, wanda ya shigar da karan, Chif David Sabo Kente yace ya fara tattaunawa da Lauyoyinshi kan hukuncin da Kotun ta yanke kafin sanin matakin da zasu dauka nan da yan kwanaki kadan.

Tunidai Kungiyar yakin neman zaben na dantakaran, wato Bwacha Gubernatorial Campaign Council, BGCC suka cigaba da gudanar da shagul-gulan murna kan nasaran da suka samu a Kotun daukaka karan.

Labarai Makamanta