Taraba: Kotu Ta Tabbatar Da Kefas Agbu A Takarar Gwamna Na PDP

Kotun daukaka kara dake da zamanta Yola, a Jihar Adamawa ta tabbatar da Laftanar Kanar Kefas Agbu (ritaya) a matsayin dantakaran Gwamnan PDP a Taraba.

Hukuncin na zuwane biyo bayan karan da Farfesa Jerome Nyameh ya shigar yana mai kalubalantan hukuncin Babban Kotun Gwamnatin Tarayya dake da zamanta a Jalingo yanke na tabbatar da Kefas a matsayin sahihin dan takaran Gwamnan Jihat Taraba a Jam’iyyar PDP

Kotun daukaka kara dake Yola, ta kara fatali da karan da Hilkiah Bubajoda Mafindi, daya daga cikin wanda aka fafata zaben fidda gwanin PDP dashi ya shigar yana kalubalantar matsayin Kefas Agbu da PDP ta tsayar a matsayi dantakarata na Gwamnan a Taraba.

Hukuncin ya kara da cewa, hukuncin Babban Kotun dake Jalingo ta yanke na tabbatar da sahihancin Kefa a matsayin dantakaran Gwamnan PDP a Taraba yayi daidai da tsari. A don da haka itama Kotun daukaka kararan tabi sahun Babban Kotun na kara tabbatar hukuncin.

Labarai Makamanta