Tambuwal Ya Dace Da Najeriya Ba Tsoffi Ba – Matasan Arewa Maso Gabas

Daga Adamu Shehu Bauchi

Hadaddiyar Kungiyar matasan Arewa Maso gabashin Najeriya sun bawa Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal wa’adin wata daya 1 da ya fito fili ya bayyana aniyarsa na takarar shugabancin Najeriya a zaben gama gari dake tafe na shakarar 2023 ko kuma su dirka shi a kotu.

Kungiyar ta fadi haka ne a wani taron da ta kira dukkan yayanta kan wan nan bukatar tasu ta bakin Shugaban Kungiyar ta kasa Engr. Ayuba Karofi.

Ya ce lokaci yayi da za’aba ma masu hazaka da hangen nesa dama ta fannin shugabanci ya shugabanci Najeriya a daidai wan nan mawuyacin halin da ake ciki a kasar

Kana yace dukkan daukacin matasa Mata da maza mun amince min gamsubda salon mulkin Tambuwal a Jihar Sokoto, ya Kara da cewa duk Najeriya a halinyanzu babu Wanda zai hada kanshi da Tambuwal, cewa chan-chantarsa a fili take.

Yana basira sosai, “Yayi dan’majalisar tarayya inda ya zama kakin majalisar kuma ya bada gumuwar sosai a lokaci, ga shi Kuma cikakken masanin shari’a a matsayin da na kwararren lauya, kana ga shi a halin yanzu shi Gwamna me karo na biyu, don haka babu Wanda zaiyi kafada dashi ta wajen zamowa shugaban kasan Najeriya” ya fada.

Karofi ya kara da cewa min gaji da mulkin tsofaffi a Najeriya domin suna rasa tunani mai kyau da zai kawo ci gaban kasa mai ma’ana, yace salon mulkin tsofaffi bashi Najeriya take so ba a halin da ake ciki na fama da wahala na tattalin arziki ga uwa uba tsaron rayukan al’umma.

Da take nata tsokacin Shugaban Mata Hajiya Aisha Baturiya yace kwansubda kwarkwatarsu suna goyon bayan wannnan bukata nan Kiran Waziri Tambuwal ya fito takarar shugabanci kasan nan a dubu biyu da ashirinnda uku, yace mata da matasa wan nan karo nasu ne, tsofaffin nan ya kamata su basu wuri.

Ta kara da cewa mu mata da matasa Mike Shan wahala wajen zabe tare da jajircewa don haka mun shirya tsaf har in Tambuwal bai fito takarar ba zamu rattaba shi a gaban koto, dolensa at fito ya cece kasar nan, ya bada tasa gudunmuwa ta fuskan shugabanci na gari da Najeriya tarasa, tace Najeriya babu abun da ta rasa nanarziki Kama daga al’umma zuwa na maadinan kasa da dai sauransu.

Labarai Makamanta