Tallafin Mai: Za A Rabawa ‘Yan Najeriya Dubu Biyar-Biyar

Labarin dake shigo mana daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya na bayyana cewar Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce za ta raba wa ƴan Najeriya tallafin sufuri na naira 5,000 a madadin tallafin mai da za ta janye gaba ɗaya zuwa 2022.

Ministar kuɗin ƙasar Zainab Ahmed Shamsuna ce ta bayyana haka a ranar Talata a wani taron Bankin Duniya kan ci gaban Najeriya.

Ministar ta ce adadin waɗanda za su amfana da tallafin ya dogara ne da yawan abin da ke hannu bayan janye tallafin.

“Kafin kammala janye tallafin mai a tsakiyar 2022, muna aiki tare da abokan hulɗarmu kan matakai da suka kamata na rage tasirin janye tallafin ga talakawa.”

“Ɗaya daga cikin matakan shi ne tsarin biyan tallafin sufuri ta hanyar tura wa ƴan Najeriya tsakanin miliyan 30 zuwa 40 kuɗi,” in ji ta.

Alƙalumman Bankin Duniya sun nuna cewa kashi 40 na talakawan Najeriya, kashi uku kawai na fetur suke amfani da shi a ƙasar, tare da nuna cewa masu arziki ne suke amfana da tallafin mai da gwamnati ke biya.

Labarai Makamanta