Tallafin Korona: Mun Raba Miliyan 25 Ga ‘Yan Najeriya – Gwamnan Babban Banki

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa yunkurin da kamfanoni masu zaman kansu sukayi na raba kayan tallafin Koronan bilyan 25 ya taimakawa talakawa sosai a lokacin da aka yi zaman dirshan na kullen Korona.

Gwamnan Babban bankin ya bayyana hakan ne a shirin kaddamar da wani Fim mai suna ‘Unmasked’ ranar Juma’a a jihar Legas. Emefiele, wanda ya samu wakilcin mukaddashin diraktan sadarwa na CBN, Osita Nwamsobi, ya bayyana cewa wadannan kamfanoni masu zaman kansu sun hada cibiyoyin killace masu Korona 39 a fadin tarayya.

Yace, “Akan wannan mun bada bashin N83.9bn ga kamfanonin hada magani da Likitoci, kuma hakan na taimakawa wasu ayyukan bincike 26 da samar da magani 56 a fadin tarayya.”

“Hakazalika mun samu nasarar janyo hankalin masu ruwa da tsaki a Najeriya ta gamayyar CACOVID, wanda hakan ya taimaka wajen samar da kayan tallafin N25bn ga gidajen da annobar ta shafa da kuma kafa cibiyoyin killace masu cutar guda 39 a fadin tarayya.”

Wadannan kamfanoni da suka bada gudunmuwa sun hada da Dangote, BUA, bankin Access da sauran su.

Labarai Makamanta