Tallafin Fetur: NNPC Za Ta Samar Da Motocin Haya Ga ‘Yan Najeriya

Labarin dake shigo mana yanzu daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), ya ba kamfanin Innoson Vehicle Motors (IVM) kwangilar kera wasu nau’ikan motocin bas na Gas (CNG) don magance illar cire tallafin mai a shekara mai zuwa.

Shugaban kungiyar Innoson, Cif Innocent Chukwuma ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Nnewi dake jihar Anambra.

“Ina kera wa NNPC motocin bas na birni. Wadanda za su yi amfani da iskar gas. Cikin rukuni 100. Ina kera su tun daga farko har karshe. Gas ne zalla.

“Amma ina yin su ne ta yadda idan aka samu karancin iskar gas za su iya amfani da dizal. Don haka, yana iya canzawa a matsayin zabi.”

Ya kara da cewa: “Zan iya kera motoci masu amfani da wutar lantarki kuma in mai da iskar gas a madadin mai. Ina so in fara kera motoci masu amfani da wutar lantarki, amma har yanzu Najeriya ba ta shirya ba.

“Duk lokacin da Najeriya ta shirya, zan samar da su. Na yi nazari kuma na horar da mutane a kai. Wannan ci gaba ne mai kyau kuma a shirye muke mu yi shi”.

Labarai Makamanta