Tallafin CORONA: Zamu Rabawa Jihohi Naira Bilyan 200 – Ministar Kudi

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa jihohin Najeriya sun samu tallafin Dala Biliyan 1.5 daga bankin Duniya na tallafin cutar Corona virus.

Ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka ga manema labarai a ganawar da ta yi da su jiya Alhamis bayan ganawar da kwamitin tattalin arziki ya yi.

Ministar Ta bayyana cewa bankin Duniyar ya lura da cewa akwai matsalar tattalin arziki dake fuskantar Najeriya, dan hakane ya ce zai baiwa Jihohin Dala Biliyan 1.5.

Ta kara da cewa ana tsammanin zuwa nan da watan Satumba za’a Rabawa jihohi 36 na kasarnan Naira Biliyan 150 zuwa 200.

Tace Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki da ba’a taba ganin irinsa ba inda tace kuma matsalar duka Duniya ce.

Saidai tace gwamnati na iya bakin kokarinta wajan ganin ta rage radadin matsin tattalin arzikin da ake ciki a Nigeria

Related posts