Tallafin Biliyan 600 Ga Manoma: Kayan Aiki Zamu Raba Ba Kuɗi Ba – Nanono

Ministan harkokin noma da raya karkara, Sabo Nanono, ya ce gwamnatin tarayya ta yanke shawarar kashe biliyan N600 a harkar noma domin farfrado da bangaren.

Nanono, tsohon manomi daga jihar Kano, ya ce za a narkar da kudaden ne a kan kananan manoma domin tabbatar da yalwar abinci da dorewar hakan a fadin kasa.

Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai kamfanin sarrafa takin zamani da hamshakin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya kammala ginawa a jihar Legas. Kazalika, Nanono ya gana da sauran ma su kamfanonin sarrafa taki da ke Legas domin ganin yadda za a samu hadin kai a tsakaninsu domin tabbatar da yalwar taki a fadin kasa.

A cewar Nanono, rabon tallafin biliyan N600 da za a bawa kananan manoma zai fara da manoma miliyan 2.4 a rukuni na farko.

Ministan ya bayyana cewa domin tabbatar da cewa ba a ci kudin gwamnati a banza ba, tallafin kayan aiki kawai za bawa manoma ba kudi ba, kamar yadda aka saba a baya.

Nanono ya kara da cewa rufe iyakokin kasashen duniya da aka yi sakamakon barkewar annobar korona ya nuna cewa Najeriya za ta iya ciyar da kanta ba tare da wani tashin hankali ba.

Labarai Makamanta