Talauci Ya Sa Ni Yin Karyar An Sace Ni – Pastor Bitrus

Wani Fasto dan jihar Filato Jos, Bitrus Albarka, wanda aka kama ranar Laraba kan zargin yin garkuwa da kansa ya bayyanawa ‘yan sanda dalilin da ya sa yayi hakan. Bitrus yace ya shirya hakan ne domin samun kudin biyan wasu bukatunsa.

Hukumar yan sandan jihar ta ce bincike ya nuna cewa Fasto Albarka na cocin ECWA ya hada kai da wasu don sace shi sannan su karbi kudin fansa.

rahoton PremiumTimes. KARA KARANTA WANNAN Bishop Kukah Ya Magantu, Ya Fadi Abun da Babban Hadimin Buhari Ya Fada Masa Bayan Ya Caccaki Fadar Shugaban Kasa

Yayin bayyanashi ga manema labarai ranar Alhamis, faston ya yi nadamar abin da yayi. Yace: “Na cusa kaina cikin harkokin nan ne saboda ina fama da wasu matsaloli na kudi. Da nayi na farko na tsargu. Lokacin da na fita kudin suka kare. Sai na sake yi. Ina nadamar abinda nayi.”

“Gaba daya na rikice. Ban san abinda ya hau kaina ba. A matsayina na fasto, ina mai bada hakuri bisa abinda na aikata. Ayi hakuri.”

Hukumar ‘yan sandan jihar a jawabin da ta fitar ta ce faston ya karbin kudi N400,000 ranar 14 ga Nuwamba, 2022, sannan kuma a ranar 30 ga Nuwamba ya sake shirya garkuwa da hakkan kuma ya karbi N200,000 wajen mambobin cocinsa.

“Ya shirya saceshi na karya ranar 14/11/2022 da 30/11/2022 inda mabiyansa suka biya Dubu dari hudu (N400,000) da Dubu dari biyu (N200,000), hakan yasa aka fara zarginsa.”

Labarai Makamanta