Takin Zamani Na Dangote Zai Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa – Dangote

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa samar da ma’aikatar Taki ta Dalla Biliyan 2 da kamfanin zai samar a yankin Lekki Jihar Legas, zai taimaka wajen habaka ayyukan noma da bunkasa tattalin Arzikin Kasa.

Ya kara da cewar ma’aikatar zata taimaka matuka wajen samar da ayyukan yi ga Matasa masu yawa, da taimaka wa Gwamnati ta bunkasa ayyukan noma da samar da abinci ga ‘yan Najeriya.

Dangote wanda ya samu wakilcin babban Darakta na kamfanin Injiniya Ahmad Mansur a rana ta musanman da aka ware wa Kamfanin a Cibiyar baje Koli ta Kasuwar Duniya da ke kaduna, yace ko shakka babu samar da ma’aikatar Takin zai taimaka wajen rage talauci da bunkasa harkar samar da abinci ga ‘yan kasa.

Da yake jawabi Shugaban Dakarun Sojin Najeriya Janar Buratai ya yabawa Aliko Dangote bisa ga kokarin da yake yi na rayawa da ciyar da Kasa gaba, “Lallai wannan abin a yaba ne” inji shi

Hakazalika mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris da sauran ‘yan Majalisar shi, sun yaba gami da jinjina ta musanman ga kokarin Kamfanin na Dangote ta fuskar samar da ayyukan yi ga Matasa.

Ma’aikatar Taki ta Dangote ta tanadi dukkanin abubuwan da ake bukata ta hanyar samar da ingantaccen taki a Najeriya domin samar da wadataccen abinci ga Jama’a, inji Injiniya Ahmed Mansur.

Lokacin da take jawabi a yayin bada lambar girmamawa ga Dangote, shugabar Cibiyar kula da Kasuwar baje Kolin ta Duniya dake kaduna Hajiya Fareeda DanKaka, ta bayyana Dangote a matsayin maceci wanda ke ceton Jama’a da tsamo rayuwarsu daga halin kaka ni kayi.

Related posts