Takardun Bogi: Gwamnatin El Rufa’i Za Ta Sallami Malaman Makaranta 233

Labarin dake shigo mana yanzu daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Nasir El-Rufa’i ta sanar da cewa za ta sallami Malaman makaranta 233 bisa gabatar da takardun bogi.

Shugaban hukumar ilmin kananan makarantun jihar SUBEB, Tijjani Abdullahi, ya sanar da hakan ranar Alhamis, 2 ga Disamba, a hira da manema labarai.

“Kawo yanzu, an tantance takardu 450 ta hanyar tuntubar makarantun da suka bada. Makarantu 9 cikin 13 sun bamu amsa.”

“Amsoshin da muka samu sun nuna cewa Malamai 233 sun gabatar da takardun bogi. Jami’a daya ciki tace takardu 212 na bogi ne.”

“Hukumar za ta sallami Malaman 233 yayinda aka tura sunayensun ma’aikatar Shari’a domin gurfanar da su kan laifin zamba.”

Shugaban hukumar ya kara da cewa a yau Alhamis za’a daura sunayen wadannan Malamai 233 a shafi yanar gizo don kowa ya gani.

Labarai Makamanta