Takarar Shugabancin Kasa: Muna Tsimayin Tinubu – Tinubu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya bukaci ‘yan Najeriya da su saurara har zuwa watan Janairu 2022 domin jin ta bakin jagoran jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, Bola Tinubu, kan ko zai yi takarar shugaban kasa a 2023 ko a’a.

Fashola ya bayyana hakan ne a wani shirin Channels TV a ranar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba inda ya yi ƙarin haske da fashin baƙi akan siyasar Najeriya.

A yan kwanakin nan, an gano fastocin Tinubu inda ake rade-radin yana neman takarar kujerar shugaban kasa a manyan birane ciki harda Lagas da Abuja. Koda dai Tinubu bai fito ya ayyana aniyarsa na takarar kujerar ba a 2023, akwai rahotanni da alamu da ke nuna cewa watakila yana da ra’ayin neman kujera.

Wasu kungiyoyi da mutane sun kuma bayyana cewa baya ga Tinubu, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, da Fashola za su iya rike Najeriya.

Da aka tambaye shi kan ko yana da ra’ayin zama shugaban kasar Najeriya, Fashola ya ce: “Babban aiki ne, mai matukar wahala; bana yiwa wadanda suka riki mukamin bakin ciki kuma bana yi wa wadanda ke takara bakin cikin samun shi.”

Kan ko zai yi magana da yawun wani dan takara a 2023, ministan ya ce:

“A iya sani na, babu wanda ya fadi cewa, ‘ina so na zama shugaban kasar Najeriya’. Akwai mutanen da ke ciwa mutane albasa. Babu wanda ya fito, Ba mu kai wannan matakin ba tukuna.

“Ina iya fitowa na ce zan yi magana da yawun wane ko wane. Ku bari mai shi ya fito ya fadi da bakinsa, ‘ina so na yiwa Najeriya hidima.’

Kan ko zai marawa takarar shugabancin Tinubu na 2023 da ake ta rade-radi, tsohon gwamnan na Lagas ya ce: “Na gan shi a makon da ya gabata, bai fada mani cewa zai yi takarar kujera ba kuma a iya sanina a jawabin karshe da yayi a kai ya ce mutane za su sani a watan Janairu.”

Labarai Makamanta