Takarar Majalisa: Rarara Ya Yi Mini Shigo-Shigo Ba Zurfi – Alan Waka

Mawaki Aminu Alan Waƙa ya fice daga jam’iyyar ADP ta Sha’aban Ibrahim Sharaɗa, sannan ya yi wurgi da takarar majalisar tarayya da yake yi a ƙaramar hukumar Nassarawa.

A cikin saƙon bidiyon da ya fitar, Ala ya nuna yayi danasanin fitowa ya bayyana kansa a matsayin ɗan takarar, domin ya ce babu wata takardar shaidar cewa yana takara da ya gani.

Ya kuma zargi ƙungiyar 13×13 da mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ke jagoranta, wanda babban jigon ADP ne a Kano da yi musu angiza mai kantu ruwa kan shiga jami’yyar bisa sharaɗi.

Sai dai ya ce, daga baya ƙungiyar ta kasa yin kataɓus domin sanar da su matsayarsu, kurum an barsu da magana da wadanda ba su da hurumi.

Ala ya ce, tuni ya aike wa jami’yyar takardar sallama.

Daga Freedom Radio

Labarai Makamanta