Taimakon Matan Da Suka Rasa Mazajensu Jahadi Ne – Gwamnan Gombe

Rahotanni daga Jihar Gombe na bayyana cewar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar ya jaddada muhimmancin tallafawa matan da suka rasa mazajen musamman iyalan jami’an tsaro waɗanda suka mutu a bakin aiki.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi wannan jawabi ne a safiyar Alhamis, yayin kaddamar da wani littafi wanda Hajiya Hassana Abubakar ta rubuta a karkashin kungiyar matan ‘yan sanda, POWA.

Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe ya bayyana hakan a jawabin da ya saki. A cewarsa, taron ya samu halartar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, wacce ta samu wakilcin Mrs Lauretta Onochie da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Baba Alkali.

Hakazalika gwamnonin jihohin Kebbi da Neja duka sun samu wakilci da ‘yan majalisar tarayya da sarakunan gargajiya da sauran fitattun mutane.

Gwamna Inuwa, ya bukaci Al ummah da su ci gaba da kula da baiwa matan da mazajensu suka rasu fifiko a yayin ayyukansu dama sauran marasa galihu.

“Nazo wannan taro da kaina ne don nuna goyon baya ga POWA, da ‘yan sandan Najeriya musamman ga dan uwana kuma abokina sufeta janar na yan sandan Najeriya, wanda na san shi tun 1982 muke abota tare da wani abokin mu, Lamido Ahmed, wanda yanzu ya rasu, don haka wannan taron zai bamu damar taimakawa domin ni da Babban Sifeta mun yi rashin aboki, masoyi wanda ya rasu ya bar iyalai”.

“Kun san a cikin al’ummar mu, al’adu, addini a wassu bangarori kuma al’amuran da suka shafi al’umma galibi suna haifar da damuwa ga matan da suka rasa mazajensu, amma a matsayin mu na masu imani dole ne mu tashi tsaye wajen sauke nauyin daya rataya a wuyan mu don taimakawa wajen rage wahalhalu gare su da ’ya’yansu.”

Ya kuma yabawa marubuciyar, Hajiya Hassana Abubakar, wacce ita ma ta rasa mijinta kuma tana da ‘ya’ya tara bisa yadda ta fito da matsalolin marasa aure a cikin al’umma da kuma bayyana irin tallafi na musamman da suke bukata dama baiwa jama’a damar yin tunani da nazari a kan su.

Labarai Makamanta