Tafiyar Atiku Turai Ta Haifar Da Surutai

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar awanni kadan bayan sanar da tafiyar ɗan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Abubakar Abubakar zuwa turai wani taro mai muhimmanci surutai sun karaɗe Jama’a.

Rahoton da muka samo daga jaridar Vanguard ya ce, Atiku zai tafi turai ne domin halartar wani zama na harkallar kasuwancinsa. Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da hadimin Atiku, Mazi Paul Ibe ya fitar ya ce mai gidan nasa zai tafi turai bayan kammala wani zama da masu ruwa da tsaki na Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) tare da abokin takararsa gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.

“Tafiyar ci gaba ce ga tafiyar kasuwancin farko a makwanni 3 da suka gabata. “A karshen tafiyar ta Turai, tsohon mataimakin shugaban kasar zai kuma yi amfani da damar don ziyartar ahalinsa a Dubai. “Tafiya dai ta kasuwanci da kuma ganawa da ahali kuma ba ta da alaka da batun lafiya kamar yadda wasu ke yadawa.”

Labarai Makamanta