Tabarbarewar Tsaro: Buhari Ba Ya Runtsawa – Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban Ƙasa, ta yi martani da bayyana kakkausan harshe dangane da zargin da ake yi wa shugaba Buhari na nuna halin ko in kula akan tsaro a yankin Arewa.

Mai ba Buhari shawara kan yaɗa labarai Garba Shehu ya bayanin irin ƙoƙarin da gwamnatin Buhari ke yi wajen ganin an magance matsalar tsaro.

“Ina tabbatar muku sakamakon halin da ƙasa ke ciki yanzu musamman yankin Arewa mai girma Shugaban ƙasa bai iya runtsawa sosai, kullum yana cikin nazari da biyu bibiyar hanyar da za a lalubo wajen magance matsalar”.

Garba Shehu ya yi bayanin irin ƙoƙarin da gwamnatin Buhari ke yi wajen ganin an magance matsalar tsaro. Sannan kuma ya bayyana yadda lamarin ba tun yau ya zama murɗaɗɗe ba.

Haka kuma ya tunatar cewa matsalar ‘yan bindiga ta zama ruwan-dare a Afrika ta Yamma, musamman daga Burkina Fasso, Mali, Nijar da wasu ƙasashen da daga can guguwar bala’in ta bugo zuwa Arewacin Najeriya.

Shehu ya yarda akwai matsalolin, amma kuma ya nuna yadda ake ƙoƙarin kawar da su, kamar yadda ya ce an kusa cin ƙarfin Boko Haram.

Labarai Makamanta