Tabarbarewar Tsaro: A Yi Gaggawar Sallamar Monguno – Matasan Arewa

Gamayyar Kungiyoyin Matasan arewa sun yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Buhari da ta sauya salon tsarin tsaro tare da yin gaggawar sallamar mai bayar da shawara kan tsaron kasa, Manjo Janar Babagana Monguno kan yawaitar kashe-kashe da farmakin da ake ta kai wa yankunan arewacin kasar nan.

Kungiyar wacce ta hada kungiyoyin matasan arewa karkashin uwar kungiya mai suna Northern Ethnic Group Assembly (NEYGA), a wata takarda da ta sa hannu a kai ranar Lahadi ta hannun kakakin ta, Ibrahim Dan-Musa, ta ce wannan kiran ya zama dole sakamakon tsanantar rashin tsaro a yankin arewa.

Kungiyoyin sun koka kan tsanantar kashe-kashen a yankunan arewacin Najeriya da yadda ya shafi tattalin arzikinta, sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki ƙwararan matakai wurin dakile yaduwar rashin tsaron.

Labarai Makamanta