Tabarbarewar Tsaro A Arewa Na Dagula Mini Lissafi – Buhari

Rahotanni daga Sokoto birnin Shehu na bayyana cewar Shugaban ƙasa Buhari ya ce yayin da tsaro a arewa maso gabas da kudu maso kudu ya inganta idan aka kwatanta da yadda ya ke lokacin da ya hau mulki, kallubalen a arewa maso yamma wani lamari ne daban.

Shugaban Buhari ya ce ya umurci sojoji da sauran hukumomin tsaro kada su sassauta wa duk wanda aka samu yana barazana ga tsaro da lafiya yan Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai fadar mai alfarma Sarkin Musulmi a birnin Sokoto.

“A kullum, muna damuwa da abubuwan da ke faruwa a arewa maso yamma. A lokacin da muka zo, idan ƴan Najeriya za su mana adalci, sun san an samu cigaba a arewa maso gabas da kudu maso kudu, amma a gaskiya abin da ke faruwa a arewa maso yamma yana tada min hankali.

“Mutane daga wuri ɗaya, al’ada ɗaya, suna kashe juna, suna sace kayan juna. Za mu yi iya kokarin mu kuma an bawa sojoji da sauran hukumomin tsaro umurnin kada su raga wa duk wani ɗan bindiga ko ɗan ta’adda.

Shugaban kasar wanda ya yi wa jihar jaje bisa hare-haren da yan bindiga suka kai a baya-bayan nan ya ce ‘Najeriya za ta yi nasara a yaƙin da ta ke yi a azzalumai’.

Labarai Makamanta