Ta’aziyyar Ganduje Ga Kwankwaso Ta Haifar Da Surutai

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje ya yi wa tsohon ubangidansa, Sanata Rabiu Musa-Kwankwaso, ta’aziyyar rasuwar Inuwa Musa-Kwankwaso kanin tsohon Gwamnan.

An ruwaito cewa, sakon ta’aziyyar na kunshe a wata takarda da kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba, ya fitar a ranar Talata a Kano mai ɗauke da sa hannun Gwamnan.

Ganduje ya kwatanta mutuwar Injiniyan aikin noman da babban rashi ga ‘yan uwansa, jiha da kasar baki daya, duba da irin kwazo da kwarewar da yake da ita.

“Ya kebance kansa a matsayin ma’aikacin gwamnati mai sadaukarwa kafin ya yi murabus, ballantana lokacin da ya yi aiki a shirin gandun daji inda ya kwashe shekaru masu yawa,”.

Ganduje ya yi fatan Allah ya sanya Inuwa a Aljanna kuma ya bai wa iyalansa hakurin jure wannan rashin.

Sai dai bayan wannan ta’aziyyar da Ganduje ya kai wa Kwankwaso, Kanawa da sauran jama’a sun shiga maganganu akai, amma a zantawar shi da BBC Hausa, Rabi’u Kwankwaso ya bayyana cewar bai damu da kowace irin niyya da Ganduje yazo da ita ba, amma komai lokaci ne abin da ka shuka shi za ka girba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply