Ta’asar Da Ake Zargin Magu Da Tafkawa

Duk da cewa hukumar DSS ta musanta rahoton cewa ta damke mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC, na tsare a ofishin yan sanda kuma a nan ya kwana.

Da misalin karfe 10:15 na dare bayan kwamitin binciken fadar shugaban ta kammala yiwa Ibrahim Magu tambayoyi, jami’an yan sandan sun yi awon gaba da shi ne daga fadar shugaban kasa.

Ga wasu daga cikin tuhume-tuhume da ake yiwa Ibrahim Magu kamar haka:

  1. Tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato hannun barayin gwamnati
  2. Ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn
  3. Rashin biyayya ga ofishin Antoni Janar na tarayya
  4. Rashin gabatar da isassun hujjoji domin dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya
  5. Bata lokaci wajen binciken kamfanin P&ID wanda ahakan ya kai ga rikicin da ake a Kotu yanzu
  6. Kin bin umurnin kotu na sakin asusun wani tsohon diraktan banki kimanin N7bn

Da dai sauran su….

Labarai Makamanta