Ta’addanci: Boko Haram Sun Kai Hari Sansanin ‘Yan Gudun Hijira

Mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram sun kashe a kalla rayuka 16 a wani hari da suka kai sansanin ‘yan gudun hijira da ke arewacin kasar Kamaru, wani jami’i ya sanar.

“A halin yanzu yawan wadanda suka rasu sun kai 16, har yanzu ba a tabbatar da cewa ko Boko Haram bace da alhakin harin ba,”

Wani mai suna Mahamat Chetima Abba ya sanar da cewar bayan harin tsakar dare da aka kai wa sansanin Nguetchewe. Wani dan siyasa da ke yankin ya kwatanta jama’ar wurin da irin mutanen da ke boyewa idan maharan Boko Haram sun bayyana.

Kungiyar ‘yan ta’addan da ta samo asali daga yankin arewa maso gabas na Najeriya tun 2009 ta saba kai hari tun a 2014. Suna kai hari wurare da dama don satar dabbobi da kayayyakin abinci.

“A makwanni kadan da suka gabata, an samu zaman lafiya amma daga baya sun yi amfani da ilimin sanin hanyar idan suka tsallake jami’an tsaro. Sun bamu mamaki.

Labarai Makamanta