Ta’addanci: Al-Ƙa’idah Sun Shigo Arewa Maso Yammacin Najeriya – Amurka

Gwamnatin kasar Amurka ya bayyanawa duniya cewa mambobin kungiyar yan ta’addan Al-Qa’ida sun fara ratsawa jihohin Arewa maso yammacin Najeriya.

Kwamandan Sojin Amurka na harkoki na musamman a nahiyar Afrika, Dagvin Anderson, wanda ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai ya ce kungiyar na shiga wurare daban-daban a yammacin Afrika.

A jawabin da TheCable ta samu daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Anderson ya ce Amurka za ta cigaba da hada kai da Najeriya wajen raba bayanan binciken sirri. Jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sune: Kaduna, Kano, Katsina, Jigawa, Zamfara, Kebbi, da Sokoto.

Muna hada kai da Najeriya kuma zamu cigaba da hadawa wajen raba bayanan sirri da wajen fahimtar abubuwan da wadannan yan ta’addan ke yi.

Kuma hakan ya taimaka musu wajen ayyukansu a jihar Borno da kuma Arewa maso yammacin Najeriya da muka ga yan Al-Qa’ida sun fara shiga.

Amma matsayinmu na al’ummar kasashen duniya, mu kan yi tunanin mun kawar da su ne kuma suna gab da wargajewa.

Ina tunanin bayan shekaru 20 mun gano cewa suna da taurin kai, duk da kanana ne, suna amfani da kafafen sada zumunta wajen daukan sabbin mambobi kuma suna samu.

Yace Anderson ya ce abinda zai sa kokarin kasashen duniya ya haifi da mai ido shine idan gwamnatin Najeriya da kanta tayi hobbasa wajen gudanar da yaki.

Labarai Makamanta