Ta’addanci: Ƙarya Muka Yi Wa Pantami – Daily Independent

A karshe dai, Hukumar gudanarwa ta kamfanin Jaridar Daily Independent ta ba Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Pantami hakuri kan labarin da ta wallafa na cewa yana cikin wadanda kasar Amurka ke zargin da alaka da ta’addanci.

Editan Jaridar ne ya bayyana haka a cikin wata wallafa ta musamman da suka yi inda ya bayyana cewar bayan gudanar da bincike sun gano cewa labarin ba gaskiya bane don haka tana ba Sheikh Pantami Hakuri kan ɓacin sunan da hakan ya jawo masa.

Jaridar tace Sheikh Pantami baya cikin wanda aka saka cikin jerin da ake zargi da ta’addanci a kasar Amurka.

Labarai Makamanta