Taɓarɓarewar Tsaro: Sojoji 356 Sun Aike Wasiƙar Neman Ajiye Aiki Ga Buratai

Wasu dakarun sojin Najeriya sun aike da wasika zuwa ga shugaban dakarun soji Janar Buratai, inda suka nemi ajiye aikin su sakamakon yadda halin tsaro ke cigaba da tabarbarewa a kasar.

Kamar yadda Jaridar WazobiaReporters ta ruwaito ta bayyana cewar kimanin dakarun soji 356 dake yankin Arewa maso Gabas suka aike da wasikar tasu ga Buratai inda suka sanar da shi aniyarsu ta ajiye aikin biyo bayan sukurkucewa da harkar tsaro ta yi a kasar.

Dakarun Sojin sun aike da wasikar tasu ne a ranar 3 ga watan Yuli na wannan shekarar ta 2020.

Amincewar aje aikin dakarun Sojin 356 ta samu sanya hannun Buratai a shafi na 17 na kundin tsarin rundunar mai lamba AHQ DOAA/G1/300/92 dauke da sanya hannun Birgediya Janar T.E Gagari ga a madadin shugaban dakarun soji, kuma ta shiga hannun wakilin majiyarmu a ranar Asabar.

Haka zalika kwafe na takardar an aike dashi Cibiyar tsaro ta Operation Lafiya Dole da ke Jihar Borno.

Majiyarmu ta bayyana cewar mafiyawan sojojin da suka aike da wasikar na cikin dakarun sojin ƙasar dake yankin arewa maso gabas inda suka koka da rashin makaman yaƙi da kula da jin dadin su, lamarin da ya sanya a kusan kullum Boko Haram ke ƙara samun galaba a kansu.

Tun a farkon wannan shekarar ta 2020 mayaƙan Boko Haram ke samun galaba akan rundunar sojin, lamarin da ake ganin ba ya rasa nasaba da sakacin shugabannin dakarun sojin wajen kula da hakkokin ƙananan dakarun sojin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply