Majalisar tarayya ta umarci kwamitin sadarwa da ya gayyaci ministan sadarwa, Dr Ali Isa Pantami, don ta fahimtar dashi bukatar samar da mafita a kan tsaro ta ma’aikatarsa.
Kamar yadda takardar sanarwar ranar Laraba tazo, wacce Ezrel Tabiowo, mai bayar da shawara na musamman ga shugaban majalisar tarayya a kan yada labarai yace, an yanke wannan shawarar ne saboda ganin halin rashin tsaro da ke addabar Najeriya.
A cewar sanatan, matsaloli irin na garkuwa da mutane, fashi da makamai, kisan kai da sauran ta’addancin da Najeriya take fuskanta sun yi yawa, mafi muni a tarihin Najeriya.
“Kisan shugaban APC na jihar Nasarawa da sauran kashe-kashen mutane da aka yi a kasar nan yana nan a cikin zuciyarmu.” Ya kara bayyana damuwarsa a kan yadda yakamata a ce wadanda suke kula da rayukan jama’a suka fara taimakon ‘yan ta’adda.
Abu mafi tsoratarwa shine yadda ake ta kama jami’an tsaro da dama masu hannu dumu-dumu a kan fashi da makami da garkuwa da mutane a cikin kasar nan.
A Najeriya ne kadai ba a yin amfani da harkar sadarwa wurin gano mutane. Ya daga maganar yadda ‘yan ta’adda suke amfani da waya wurin tattaunawa da iyaye da ‘yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su, kuma su amsa kudi ba tare da an kamasu ba, ta yaya za a yi a ce ba a amfani da irin wannan damar wurin damkarsu?